Ya zuwa ranar 29 ga Oktoba 2022, Ma'aikatar Uganda Hukumar lafiya ta kasar ta bayar da rahoton mutane 128 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan 34 sun mutu.
Dangane da bayanan da ake da su da kuma kimanta hadarin da aka gudanar, Najeriya na cikin babban hadarin shigowa da kwayar cutar.
NCDC ta ce ganin yadda ake yamutsa fasinjojin kasashen Najeriya da Uganda a filayen jirgin sama tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cakuduwar fasinjoji, musamman a wuraren tafiye-tafiye na yankin Nairobi, Addis Ababa, da filayen tashi da saukar jiragen sama na Kigali, akwai matukar hadarin yiwuwar cutar ta shigo Abuja cikin sauki.
Hukumar ta ce tuni ta dauki matakan kariya don ganin ba a samu yaduwar cutar ba, yayinda sashen na tunkarar annoba ke cikin shirin ko ta kwana don fara ayyukan shirye-shirye a cikin ƙasa.
Matakan rigakafin don rage tasirin yiwuwar bullar cutar ta EVD a Najeriya sun hadda da bin sawun fasinjojin da suka taho daga Uganda da wadanda suka yi tafiya zuwa kasar Uganda tsawon kwanaki 21 bayan sun isa Najeriya.