Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda Ta Kulle Gundumomi 2 A Kokarin Dakile Yaduwar Cutar Ebola


Daya daga cikin gundumomi biyu da aka kebe.
Daya daga cikin gundumomi biyu da aka kebe.

Hukumomin Uganda sun sanya dokar hana zirga-zirga a wasu gundumomi biyu da cutar Ebola ke ta yaduwa a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.

Matakan da shugaba Yoweri Museveni ya sanar na nufin mazauna yankunan Mubende da Kassanda na tsakiyar Uganda ba za su iya shiga ko fita daga yankunan ba. Za a bar motocin dakon kaya da sauran su da ke wucewa daga Kampala babban birnin kasar, zuwa kudu maso yammacin Uganda su su cigaba da aiki, in ji shi.

Hukuman kiwon lafiya
Hukuman kiwon lafiya

An ba da umarnin rufe dukkan wuraren nishadi gami da wuraren sayar da giya , da wuraren ibada, kuma duk wata jana’iza a wadannan gundumomin dole ne jami’an lafiya su sa ido a kan su. An kuma sanya dokar hana fita da dare. Kullen zai dauki akalla kwanaki 21.

"Wadannan matakai ne na wucin gadi don shawo kan yaduwar cutar Ebola," in ji Museveni.

Cutar Ebola ta kama mutane 58 a kasar dake gabashin Afirka tun daga ranar 20 ga watan Satumba, lokacin da hukumomi suka sanar da bullar cutar. Akalla mutane 19 ne suka mutu, ciki har da ma’aikatan lafiya hudu. Hukumomin Uganda ba su yi saurin gano bullar cutar ba, wadda ta fara kama mutane a wata unguwa a cikin watan Agusta " a cewar hukumomin yankin.

Sabbin matakan sun zo ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa wasu majinyata a wuraren da Ebola ta bulla za su iya neman magani a asirce a wani wuri daban kamar yadda wani mutum da ya tsere daga Mubende ya mutu a wani asibiti a Kampala a farkon wannan watan. Lamarin da ya ta da wa jami'an kiwon lafiya hankali.

Hukumomin Uganda sun tattara bayanan tuntubar mutane sama da 1,100 masu cutar Ebola, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka da Cututtuka ta Afirka. Wani nau'in cutar Ebola na Sudan, wanda ba a tabbatar da samun rigakafin shi ba, yana yaduwa a cikin kasar mai cike da mutane miliyan 45.

Ebola, wanda ke bayyana a matsayin zazzabin jini, yana da wahala a gano shi da farko saboda zazzabi ma alama ce ta zazzabin cizon sauro.

Cutar Ebola na yaduwa ta hanyar cudanya da ruwan jikin mai cutar ko gurbatattun kayayyaki. Alamomin sun hada da zazzabi, amai, gudawa, ciwon jiki da kuma wani lokacin zubar jini na ciki da waje.

Cutar ta Ebola ta fara bulla ne a shekarar 1976 a wurari biyu a lokaci guda. Da Sudan ta Kudu da Kongo, inda ta bulla a wani kauye kusa da wani kogi da ake fi sani da Kogin Ebola.

XS
SM
MD
LG