Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Wasu Mutane Dauke Da Annobar Ebola A Kasar Guinea


An samu barkewar annobar Ebola a wasu kauyuka da ke kasar Guinea.

Bayan an tabbatar da mutane uku da suka kamu da cutar Ebola a Guinea, hukumomin lafiya na yankin sun bayyana barkewar cutar a yankunan karkara na Gouéké da ke N’Zerekore a ranar 14 ga watan Janairu.

Dangane da sabon rahoton da aka samu, kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa tana hada kan wani shiri don magance barkewar cutar a Guinea.

"Daga abubuwan da suka gabata mun san cewa saurin tunkara na da mahimmanci, domin a samu dakile yaduwar cutar da kuma samar da magani ga mutanen da suka kamu da cutar," in ji Frederik van der Schrieck, shugaban ofishin kungiyar a Guinea. Ya kara da cewa, "Mun kuma san cewa, yin hulda da al'umma yana da mahimmanci."

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG