WASHINGTON, DC - Kwayoyin cutar Marburg masu saurin yaduwa da ke shafar sassan jikin bil’adama na dangin kwayoyin cutar Ebola. Alamomin cutar sun hada da gudawa, masassara, tashin zuciya da amai.
Hukumar lafiya ta duniya ta WHO ta tabbatar da sakamakon gwajin da aka yi wa wasu mutane biyu marasa alaka da juna a yankin Ashanti da ke kudancin Ghana wadanda tuni suka mutu.
Hukumar WHO ta ce tana sa ido kan mutane fiye da 90 da suka yi mu’amalla da mutanen biyu.
“Hukumomin lafiya sun mayar da martanin gaggawa, inda suka fara shirye-shiryen tunkarar yiwuwar barkewar cutar. Wannan matakin na da kyau, saboda in babu wani matakin gaggawa zai yi wuya a shawo kan cutar Marburg cikin sauki," a cewar Dr. Matshidiso Moeti, Daraktan hukumar WHO na yankin Afirka.
Ya kara da cewa jami’an WHO na Ghana don taimaka wa hukumomin lafiya, kuma yanzu da aka sanar da barkewar cutar, suna shirya duk abubuwan da ake bukata don maida martani.
Wannan shi ne karo na biyu da cutar Marburg ta bayyana a yammacin Afirka. A karon farko cutar ta fara bulla kasar Guinea a watan Satumban shekarar 2021.
Haka kuma cutar ta bayyana a Angola, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Kenya, Afirka ta Kudu da Uganda.
A yanzu dai babu rigakafi ko maganin cutar Marburg, amma WHO ta ce "kulawa mai kyau, kamar ba majiyyaci ruwa sosai ko yi masa karin ruwa ta jijiya da kuma magance takamaiman wasu daga cikin alamomin cutar, zasu taimaka wajan inganta damar rayuwar majiyyaci."