A cewar gwamnan jihar Alhaji Tanko Umaru Al-Makura yace sun yi taro da sarakunan gargajiya da jami'an tsaro kuma sun tabbatar cewa jama'a da suka gujewa muhallansu yanzu zasu iya komawa.
Gwamnan yace sun zauna da sarakuna daga kowace masarauta kuma sun basu tabbaci za'a zauna lafiya. Dalili ke nan da suke kiran mutane su koma gidajensu a garuruwansu da suka baro. Yanzu akwai hadin kai da sarakuna da jami'an tsaro. An raba kayuka da garuruwa tsakanin jami'an tsaro wadanda zasu dinga zirga-zirga. Jami'an tsaro zasu bi kowace kusurwar masarauta masarauta abun da ba'a taba yi ba.
Ta bakin gwamnan babu wurin da za'a mayar da mutane da babu jam'an tsaro. Yin hakan zai hana masu tada tarzoma zuwa wuraren.
Domin karfafa gwiwar mutanen su koma wurarensu gwamnati ta sayowa jami'an tsaro motocin hilux guda goma. Ta kuma sayo kayan gini da zata rabawa mutane domin su gyara gidajensu ko su sake ginasu da na abinci domin rabawa duk wadanda suka koma.
An Doma na Doma Alhaji Aliyu Ahmadu shi ne shugaban kwamitin sasanta al'ummomi yace yunkurin da gwamnati ta keyi na a zauna lafiya ya kaiga samar masu kayan sake gina muhallansu da suka bari.
'Yan gudun hijiran sun amince su koma to amma sai da jami'an tsaro da zasu karesu a wuraren zamansu na wani dogon lokaci. To saidai wasu sun ce har yanzu akwai wuraren da ba'a iya zuwa domin rikicin sai kara ruruwa yake yi a wasu wuraren.
A ganin wasu kamata yayi su jera da jami'an tsaro, wato ga kafafun jami'an tsaro ga nasu.
Ga rahoton Zainab Babaji.