Shugaban wanda ya fara yada zango a sansanin sojoji dake Mubi ya isa garin ne a wani tsatsauran matakin tsaro.
Daga barikin sojojin ne shugaban ya tafi fadar sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu. Amma ziyarar ta bar baya da kura.
Masana harkokin tsaro da adanda ya kaiwa ziyarar suna ganin da walakin wai goro a miya. Ma'ana, akwai wani dalili daban da ya kai shugaban Mubi duk da mahukunta basu bada bayani ba.
Mazauna garin Mubi sun ce sojoji sun hanasu fita saboda haka basu ga shugaban ba basu kuma jia jawabinsa ba. Jama'ar garin sun ce babu wanda ya san shugaban kasa zai kai ziyara garinsu. Shugaban daga barikin sojoji sai fadar sarki. Babu inda ya je kuma.
Zuwan ya ba mutane mamaki. Kowa na tambaya menene shugaban ya zo yi? Tun lokacin da aka kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram kusan watanni hudu kenan shugaban bai je ya ga mutane ba sai wannan karon. Wannan karon ma bai ga kowa ba sai sojoji da sarkin garin. Shin wai shugaban bai damu da talakawan yankin ba kenan.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz