Wani karamin bincike da aka gudanar ya nuna cewa kananan matasa dake shan taba na cikin hadarin samun ciwon rabin jiki kafin su cika shekaru 50 sabanin sa’anninsu da suka gujewa taba.
An dade ana alakanta shan taba da abinda ka iya kara hadarin samun cutar bugun jini ga tsofaffi, sai dai kawo yanzu binciken da aka gudanar an nemi alakar hakan da matasa inda aka maida hankali akan mata. A wannan bincike, masu gudanar da binciken sun bincika bayanai kan maza 615 wadanda suka sami cutar bugun jini kafin su cika shekaru 50, aka kwatanta dabi'ar shan tabarsu da wasu mutanen 530 wadanda basu taba samun cutar bugun jini ba.
binciken ya nuna cewa, kashi tamanin da takwas cikin dari na wadanda ke shan taba suna cikin hadarin kamuwa da cutar bugun jini fiye da wadanda basu shan taba.
Binciken da Janina Markidan ta jami'ar Kimiyya dake Maryland a Baltimore ta jagoranta ya gano cewa, "Abu mafi muhimmanci shine yawan shan taba ka iya kara hadarin kamuwa da cutar bugun jini.
Facebook Forum