Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce nan ba da jimawaba za ta samu nasarar kubutar da daliban Islamiyyar Salihu Tanko da aka sace a jihar Neja da ke hannunun ‘yan bindiga.
A yanzu dai wadannan yara sama da dari suna cikin makonni 11 kenan a hannun wadannan ‘yan fashin daji ba tare da samun nasarar kubutar da su ba.
A wani taron masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaron a masarautar Kontagora sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Nejan Monday Bala Kuryas ya ce sun kara shirya jami’an tsaronsu, kuma nan ba da jimawa ba za su kwato yaran.
Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana neman hadin kan jama’a musamman kabilar Fulani wajen yaki da bata garin dake cikinsu in ji kwamishinan kananan hukumomi da masarauta na jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da ya wakilci gwamnatin jihar Neja a wajen taron.
Wakilin kabilar Fulani a taron sarkin Fulanin masarautar Kontagora Hardo Abubakar Badare yace sun shirya bada rayuwarsu domin samar da zaman Lafiya a yankin.
Masarautar Kontagorar dai daya daga cikin yankunan dake fama da matsalar ‘yan fashin daji masu satar shanu da yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa dama, kisan jama’a babu gaira babu dalili.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: