Hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya NCC ta yi kira ga matasan kasar da su himmatu wajen samun kwarewa a fannin ilimin tattalin arziki na yanar gizo.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta NCC ta fitar a shafinta na Facebook, dauke da sa hannun darektan yada labaran hukumar, Dr Ikechukwu Adinde, Mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba Danbatta, ya yi kira ga matasan da suka halarci wani taron horar da matasa a wannan fanni, da su yi amfani da abin da suka koya ta hanya mai kyau.
A cewar sanarwar, sarrafa ilimin ta yin shi a aikace ta hanyar da ta dace, zai taimakawa matasa wajen samun ayyukan da za su dogara da kansu.
A karshen makon da ya gabata aka rufe wani shirin horar da matasan yankin arewa maso yammacin Najeriya a Kano a fannin tattalin arzikin yanar gizo.
“Wannan horo ya ba ku damar samun wani ilimi mai amfani, wanda zai ba ku damar dogaro da kanku ba tare da dogaro da aikin gwamnati ba.
“Fatan hukumar NCC shi ne, za ku yi amfani da abin da kuka koya ta hanya madaidaiciya ta yadda za ku koyawa abokanku da wadanda kuke hulda da su.” Sanarwar ta ce.