Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wasu Matafiya Da Dama A Jihar Filato


Gwamnan jihar Filato Simon Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)
Gwamnan jihar Filato Simon Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)

Rundunar sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar ta ce ta kama mutum 12 da take zargi da hannu a kisan matafiyan.

Rahotannin daga jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya na cewa wani gungun matasa ya hallaka wasu Fulani matafiya da dama a hanyar Rukuba Road da ke cikin garin Jos.

Lamarin ya faru ne a karshen makon nan yayin da matafiyan ke kan hanyarsau ta komawa jihar Ondo daga jihar Bauchi a lokacin da suka ratsa ta cikin yankin karamar hukumar ta Bassa.

Wasu bayanai sun yi nuni da cewa mutum 17 ne suka mutu yayin da wasu ke cewa mutum takwas.

Al’amarin ya faru ne yayin da al’umar Irigwe ke jana’izar mutanen da aka kashe a rikicin da ya auku a kwanan nan a jihar ta Filato.

Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Fulani a Najeriya Abdulkarim Bayero ya ce ya ga gawarwakin mutum 17.

“Yanzu dai da idona na kirga gawarwakin mutum 17, wadanda suka jikkata sun fi 20 domin an rarraba su zuwa asibitoci daban-daban. Gaskiya yanayin akwai bakin ciki da alhini sosai, domin wadannan mutanen ba ‘yan jihar Filato ba ne, ‘yan wasu jihohi ne suka kai wa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara.”

Ya kara da cewa, daukar fansar da ake yi yayin wani rikici ba zai magance matsalar da ake ciki ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa matafiyan suna cikin wasu motocin bas guda biyar ne kirar Hummer a lokacin da matasan suka tare su.

Sai dai shugaban matasan unguwar da lamarin ya auku, Godwin Wilson, ya ce lamarin ya fara ne da zage-zage tsakanin matasan yankin da matafiyan, har ya kai ga abin da ya faru.

“Abin ya kai ga an fara harbi da duwatsu, ni gudu ma daga wurin na yi saboda ni ban saba ganin irin wannan lamari ba.”

Rundunar sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar ta ce ta kama mutum 12 da take zargi da hannu a kisan matafiyan.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta kara da cewa, suna nan suna tatsar bayanai daga wadanda ake zargi.

A halin da ake ciki gwamnatin jihar Filato ta fitar da wata sanarwa ta hannun kakakin gwamna Simon Lalong, Makut Simon Machan wacce ta yi Allah wadai da wannan lamari, inda ta kuma nemi hukumomin tsaro da su gaggauta hukunta wadanda ke da hannu a wannan lamari.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00


XS
SM
MD
LG