NIAMEY, NIGER —
A makon jiya shirin Nakasa ya maida hankali akan wahalhalun da masu bukata ta musamman ke fama da su a Najeriya sadaniyar matakin canjin takardar Naira, inda a yanzu haka ake tafka mahawara kan wannan batu da wasu rahotanni ke cewa ya haifar da tsayawar al’amura a fannoni da dama.
To da yake a Najeriyar aski ya zo gaban goshi game da shirye shiryen babban zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, shirin ya tuntubi shugabannin kungiyoyin nakasassu don jin matsayin wannan zabe a gare su da kuma fatan da suke da shi a kai.
Saurari shirin cikin sauti: