NIAMEY, NIGER —
Gwamnatin jamhuriyar Nijar da asusun tallafin yara na Majalisar Dinkin Duniya na UNICEF, tare da hadin gwiwar kungiyoyin nakasassu sun fara naziri kan hanyoyin shimfida tsarin katin da zai bai wa masu bukata ta musamman damar samun sassauci a fannoni da dama na rayuwar yau da kullum, kamar sha’anin kiwon lafiya da sauransu.
Shugaban gamayyar kungiyoyin nakasassu Federation des Personnes Handicapees Siddo Nouhou Oumarou ya yi wa wannan shiri karin bayani bayan zaman da suka gudanar kan wannan kudiri a garin Dosso.
Saurari cikakken shirin Souley Moumouni Barma: