Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAKASA BA KASAWA BA: Ci Gaban Tattaunawa Da Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Nakasassu Siddo Nouhou Oumarou, Fabrairu 2, 2023


Souley Mummuni Barma
Souley Mummuni Barma

A yanzu haka kungiyoyin nakasassun Nijar sun dukufa wajen neman hanyoyin farfado da asusun tallafin masu bukata ta musamman wato Fond De Soutien aux Personnes Handicapees wanda mahukunta suka dakatar da shi a shekarar 2018.

Ko da yake a baya-bayan nan hukumomi sun kudiri aniyar samar da sassauci ga mutanen da ke da tawaya, musamman wadanda ke cikin mawuyacin hali. Shugaban gamayyar kungiyoyin nakasassu Siddo Nouhou Oumarou ya ce rashin wancan asusu abu ne da ya haddasa damuwa sosai, ciki har da koma bayan sha’anin ilimin nakasassu, inda wasu daga cikinsu suka fara tunanin zuwa cirani.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

NAKASA BA KASAWA BA: Ci Gaban Tattaunawa Da Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Nakasassu Siddo Nouhou Oumarou
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00

XS
SM
MD
LG