Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yana samun kwarin gwiwa kan yadda a ke ganin karin kasashen duniya suna fitowa suna kira da a cimma matsayar dakatar da bude wuta a fadan Isra’ila da Hamas.
Sai dai ya ce ya yi “mamaki da ya ga ana ci gaba da harba bama-bamai a yankin Zirin Gaza maimakon a ga sassauci.
Babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kai ziyarar ba-zata a Doha babban birnin Qatar a ranar Asabar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron yanayi da za a yi a Nepal.
Yayin ziyarar ta sa, Guterres ya gana da Firai Minista Sheikh Mohammeed Bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani inda suka tattauna kan wannan rikici.
Ita dai Qatar tana da kyakkyawar alaka da Hamas, wacce ke da ofishi a kasar.
Kazalika Qatar ta taka muhimmiyar rawa wajen sako wasu mata biyu daga Gaza, kuma rahotannin sun ce tana kokarin ganin an sako karin Yahudawan da Hamas ta kama.
Kazalika Guterres ya gana ta wayar tarho da shugaban Masar Abdel Fatah el -Sisi kan halin matsanancin rayuwa da mutane ke ciki a Gaza.
Ita dai Masar ita take kula da iyakar Rafah da Gaza.
A daren Juma’a Isra’ila ta sanar da kara fadada hare-haren da take kai wa ta kasa a Gaza tare da katse hanyoyin intanet da wayoyin tarho a yankin wanda Hamas ke iko shi.
Dandalin Mu Tattauna