Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Musunta Zarce Kowa Talauci


Al'ummar Makoko a Jihar Legas
Al'ummar Makoko a Jihar Legas

Gwamnatin Najeriya ta ki amincewa sakamakon da wani shirin bin diddigin yanayin talauci a duniya mai suna World Poverty Clock ta bayar game da Najeriya a matsayin kasar da ta fi yawan jama’ar da ke cikin kangin talauci a duniya inda a yanzu ta wuce kasar Indiyar da yawan jama’arta ya ninka na Najeriya sau 7.

Ministan zuba jari da kasuwanci na Najeriya Okecukwu Enelamah ya ce rahoton ba shi da, inganci ko ta ka yiwu an dora shi a ma’aunin lokacin da Najeriya ke cikin kangin tattalin arziki da alkaluma yanzu su ka nuna Najeriya ta fita daga wannan fatara bisa matakan da gwamnatin Buhari ke dauka.

Rahoton ya nuna Najeriya ta wuce Indiya da yawan masu fama da tsananin fatara inda Najeriya ke da sama da mutum miliyan 86 indiya kuma na da mutum miliyan 73.

Rahoton na nuna cewa, a duk minti 1 mutum 6 kan kunduma cikin tsananin talauci a Najeriya.

Wadannan yawan mutane dai ya nuna na rayuwa ne kasa da Naira 600 a wuni wato kasa da dala 1.90.

Ministan zirga-zirgar jirage Hadi Sirika ya ce Najeriya fa ta riga ta farfado daga bayanan irin wannan rahoto don farashin gangar mai ya farfado zuwa kimanin dala 70 kuma tuni an samu nasarar dakatar da fasa bututun fetur daga Neja Delta.

Manyan masana tattalin arziki na nuna gwammnatin ba ta kama hanyoyin gyara tsari da talaka zai ji a jikin sa ba kama daga kalubalen tsadar man fetur, man girki, shinkafa da ma makamashin lantarki da sauran su.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Dr.Obadiah Mailafiya na daga masu nuna irin wannan damuwa.

“Ina maganar fita daga fatara a na komawa baya dai,”inji shi

Ra’ayin mutane dai na bambanta kan kuncin talaucin na Najeriya bisa goyon baya ko adawa da muradun a muradun siyasa.

In za a tuna shugaban Najeriya ya sanya hannu kan kasafin kudin bana Naira tirliyan 9.1 da zargin majalisa da tauye wasu manyan aiyuka da cusa kananan aiyukan da su ka shafe su.

Ba shakka cece-kucen da ya ki karewa tsakanin sassan gwamnati masu hurumin dimokradiyya na wahalar da Najeriya da masu sharhi ke cewa siyasantar da lamura ke kawo matsala ba gaskiya ba ko tsananin rikon amana ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG