Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawara Kan Bashin Naira Tiriliyan 71 Da Ake Bin Gwamnatin Najeriya


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Watanni shida da cikar wa'adin mulkin shugaba Mohammadu Buhari, bincike ya nuna cewa jimlar basussuka da gwamnatin Tarayya ta ciwo da sauran lamuni da ta yi sun kai Naira triliyan 71.5 amma masana tattalin arziki sun bayyana ra'ayi mabanbanta akan haka.

ABUJA, NIGERIA - Adadin wadannan basussukan dai, ba su hada da kudaden bashi da gwamnati ke bin ma'aikatu ba, wadannan sun kunshi bashin da gwamnatin tsakiya ta ci ne, da kuma wadanda ta yi lamunin su ga jihohi, da cibiyoyi da kuma hukumomin gwamnati.

Manazarta sun ce akwai wasu basussukan da ba su da takardun shaida, kuma suna iya shiga cikin wadannan dimbin tiriliyoyin Naira da dama, haka kuma akwai lamunin kudi masu yawan gaske da gwamnati ta yi wa wasu yankunan, da Jihohi da cibiyoyi na duniya da kasar ke shiga a matsayin mamba.

Yusuf Abubakar Yusuf
Yusuf Abubakar Yusuf

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf mai wakiltan Jihar Taraba ta tsakiya kuma daya cikin 'yan kwamitin kula da kudi a majalisar Dattawa, ya yi karin haske cewa an karbi yawancin basussukan ne daga kasashen waje, kuma akwai basussukan cikin gida da kuma wadanda gwamnati ta yi lamuninsu da jimlar su ya kai Naira triliyan 71.5.

Yayin da bashin da ake bin gwamnatin tsakiya ya tashi daga Naira tiriliyan 10 a watan Yunin shekara 2015 zuwa Naira Triliyan 35.7 a watan Yunin wannan shekara da muke ciki, ya sa gwamnati ta yi bayani cewa, akwai bashin da ta ke bin ‘yan kwangilar gina tituna, da ya kai kusan Naira triliyan 11.16 amma kuma ta ce za ta himmatu wajen ganin an yi ayyukan kwangilan, musamman na tituna a shiyoyin kasar da dama.

CBN
CBN

Duk da haka, akwai takardun shaidar kamalla aiki na Naira biliyan 765 da wannan bincike ya gano cewa ba a riga an biya wadanda suka yi aikin ba.

Wanan bayani na gwamnati ya sa kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa Shu'aibu Idris Mikati ya bayyana cewa, bashi hanji ne yana cikin kowa, kuma sai kasa ta kai kasa ne ake ba ta bashi.

Sai dai Mikati ya ce matsalar da ke kawo wa Najeriya koma baya wajen samun kudaden shiga shi ne yawan sace man fetur da kasar ke hakkowa. Mikati ya ce yanzu dai za a fara samun sauki domin an dauki matakin dakile hanyoyin sace-sacen man fetur da ake yi.

To ko yaya gwamnati za ta biya wadannan basussuka ?

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce ana iya fitar da zunzurutun kudi a biya bashin, ko kuma ta hanyar lamuni ko ta abin da ake cewa BOND da DABENTURE da turanci.

Yusuf ya kuma ce, yin haka yana iya zama a cikin shekaru da dama, kamar daga shekara daya har zuwa 10 ko fiye da haka.

IMF
IMF

Asusun Lamuni na duniya IMF ya yi kira ga Babban Bankin Najeriya da ya kara kaimi ga tsarin habaka kudaden shiga domin a rage radadin talauci da hauhawan farashin kayayyakin masarufi da al'umma ke fama da shi.

Najeriya dai ta shiga wannan hali na dimbin bashi ne sakamakon satar da ba a taba ganin irin ta ba, da ake yi a bangaren man fetur wanda ta nan ne kawai Gwamnati ke samun kudaden shiga.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Muhawara Kan Bashin Naira Tiriliyan 71 Da Ake Bin Gwamnatin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG