Babban Hafsan Hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya sanar da kafa cibiyar bincike da inganta fasaha da rundunarsa ta kafa a jihar Kaduna. Cibiyar data kunshi injiniyoyin sojojin sama suka hada gwiwa da bangaren kimiyya da fasaha ta rundunar, wajen samar da cibiyar.
Yace sun taka rawar gani da dama kuma za'a nuna kadan daga cikin kayan da suka kirkiro. A cewar babban Hafsan, cibiyar ta samu nasarar gyara jiragen leken asiri marar sa matuka da suka baci watannin da suka gabata saboda rashin kayan gyara. Yanzu haka jiragen suna arewa maso gabas inda suke aiki tukuru.
Air Commodore Tijjani Gamawa masanin tsaro ne da yayi aiki a rundunar sojin saman Najeriya, yace irin shugabancin da sojojin ke dashi yanzu ne ya taimaka aka samu ci gaba. Sojojin na iya yin wasu abubuwan da ba sai an fita waje an kawo ba.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina don karin bayani
Facebook Forum