Shugabannin gidauniyar da ake kira "Complete Care" da turanci ta ce burinta ne ta taimakawa mata da marayu wadanda rikicin Boko Haram ya jefa su cikin mawuyacin hali. Akalla mutane dubu 10 ne zasu amfana karkashin shirin.
Shugabannin kungiyar suka ce zasu kuma tallafawa akalla makarantu dubu biyar.
Da suke magana da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda, shugabannin suka ce zasu sa ido kan yara wadanda suke fama da 'yunwa da karancin abinci mai gina jiki.
Shirin zai kuma taimaka wajen gudanar da shirin musayar dalibai daga sassan kasar daban daban.
Daga karshe kungiyar Complete Care ta yi kira ga sauran kungiyoyi da su shigo su taimakawa gwanati a yunkurin da take yi na sake farfado da wannan yanki.
Ga rahoton.
Facebook Forum