Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Laifi A Zabukan 2023


Hukumar INEC
Hukumar INEC

A wannan makon ne Najeriya ta fara shari'ar daruruwan mutanen da suka hada da jami’an hukumar zaben kasar da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi babban zaben kasar na bara.

An soma shari'ar mutane 190 da suka hada da jami'an hukumar zabe da na manyan jam'iyyun siyasa a gaban kotuna daban-daban na kasar a ranar Litinin.

Lauyoyi daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, ko INEC, ne ke zama masu gabatar da kara a shari’ar, inda lauyoyi daga kungiyar lauyoyin Najeriya kuma za su bada da kariya.

Hukumar ta INEC ta ce shari’ar za ta zama darasi nan gaba a zabe mai zuwa.

Godbless Otubure, wanda ya kafa kungiyar nan mai fafutukar tabbatar da dimokradiyya ta Ready to Lead Africa, ya ce kungiyoyin fararen hula na maraba da shari’ar amma suna fatan ba wai ana yi don ganin ido ba ne.

Wadanda ake tuhumar dai na fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da sayan kuri’u, sata da lalata kayayyakin zabe, rashin da’a a wuraren zabe, rashin kula da aiki da gangan, mallakar makamai da kuma tashin hankalin da ya shafi zabe.

Lamura irin haka sun zama ruwan dare a Najeriya, ko kafin zabe, lokacin zabe ko kuma bayan zabe. A babban zaben kasar na bara, 'yan sanda sun ce an kashe mutane fiye da 20 a tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe.

Bisa ga binciken Afrobarometer na gabanin kada kuri’a, kasa da kashi hudu na ‘yan Najeriya sun amince da tsarin zaben. Masu sharhi sun ce rashin bin ka’ida a lokacin zaben ya kara dagula al’amura.

Otubure ya ce idan har shari’ar ta kai ga yanke hukunci, hakan na iya sauya ra’ayin jama’a.

“Batu ne na sanadi da sakamako,” a cewar Otubure. Ya kara da cewa, “Idan mutane suka sace akwatunan zabe, suka kawo cikas wajen gudanar da zabe, kuma ba a hukunta su ba, hakan na iya rage amincewar jama’a gaba daya, idan mutane suka aikata laifukan zabe aka gurfanar da su a gidan yari, za a iya sake cusa yarda a zukatan jama'a.”

Yanzu dai kungiyoyin farar hula da masu sa ido za su ci gaba da bibiya su ga abin da zai faru

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG