Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Jingine Hukunci Kan Karar Binani Na Kalubalantar Nasarar Fintiri


Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

Kotun Koli ta jingine hukunci a karar da jam’iyyar APC da ‘yar takar gwamna a zaben da aka gudanar a ranr 18 ga Maris din 2023, Aisha Binani, wacce aka fi sani da Binani su ka shigar akan gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Kotun kolin Najeriya dake da zamanta a birnin tarayya Abuja ta jingine hukunci a karar da jam’iyyar APC da ‘yar takarar gwamnan ta, Sanata Aisha Dahiru Binani , suka shigar na kalubalantar nasarar gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

A baya dai kananan kotuna biyu da suka hada da na sauraron kararrakin zabe da na daukaka kara sun yi watsi da karar Aisha Binani da ke kalubalantar nasarar Finitiri a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Tawagar masu shari’a 5 karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ne ya jingine ci gaba da sauraren karar bayan ya saurari bahasi na bangarori biyu da lamarin ya shafa.

Babban abin da ake takkadama a yayin zaman na yau da Binani ta gabatar ta bakin lauyanta, Akin Olujimi, shi ne ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zabe mai cike da cece-kuce da kwamishinan zaben jihar Adamawa Hudu Ari ya yi.

Zaman kotun na yau kan takaddamar wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris a jihar Adamawan na zuwa ne watanni da dama bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa tare da yin watsi da karar kalubalantar nasararsa da Aisha Binani ta shigar a bisa cewa bai cancanta ba.

Haka kuma, kotun ta ci tarar dubu 500 ga Binani zata baiwa Fintiri da jam’iyyar PDP.

Wannan hukuncin ya yi daidai da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a ranar 28 ga watan Oktobar shekarar 2023 wanda ya yi watsi da karar da Binani ta shigar a bisa matsalar kasa tabbatar da zargin kada kuri’u fiye da kima ta hanyar kin gabatar da hujojji kan karar ta da ke da nasaba da sukar sakamakon zaben.

Idan Ana iya tunawa, kafin a fara cece-kucen shari’a, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna wanda ke cike da cece-kuce.

Alkaluman kididdiga daga hukumar INEC ya yi nuni da cewa Fintiri na jam’iyyar PDP ya sami jimillar kuri’u dubu 421 da 522, a yayin da babbar abokiyar hamayyarsa Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC ta sami kuri’u dubu 390 da 275 daga kananan hukumomi 21.

Haka kuma, a baya a wani mataki mai cike da cece-kuce, Hudu Ari, yayin da ake gudanar da tattara sakamakon, da wuri ya ayyana Binani a matsayin wacce ya lashe zaben wanda hakan ya sabawa tanadin sashe na 25 na dokar zabe ta shekarar 2022 wanda ya bai wa baturen zabe kawai ‘yancin bayyana sakamakon zaben gwamna.

A Waccan lokacin, nan take bayan sanarwar Hudu Ari ne hukumar INEC ta yi watsi da sanarwar, daga nan kuma ta dakatar da tattara sakamakon zaben da aka kammala a Adamawa sannan ta gayyaci babban jami’in zabe, Hudu Ari da duk jami’an da abin ya shafa da su kai rahoto zuwa hedikwatar hukumar da ke birnin Abuja.

Daga bisani dai hukumomin ‘yan sanda sun cafke Hudu Ari, inda suka tabbatar da kama shi kuma har yanzu yana gaban kotu yana fuskantar tuhuma.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG