Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Fubara Da Ahmad Da Kefas A Matsayin Gwamnonin Ribas Da Sokoto Da Taraba


Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar APC, Tonye Cole ya daukaka inda ya kalubalanci nasarar Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Ribas a bisa rashin cancanta.

A yayin tabbatar da Fubara a matsayin zababben gwamnan jihar Ribas, Kotun Kolin ta ce wanda ya shigar da karar bai tabbatar da zargin kin bin dokar zabe da dai sauransu da hujojji gamsassu ba.

Haka kuma, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben ranar 18 ga Maris na shekarar 2023, Tonye Cole ya kalubalanci nasarar Fubara na jam’iyyar PDP ne a bisa cewa bai yi murabus daga mukaminsa na akanta Janar na jihar Ribas ba kafin zaben.

Kotun daukaka kara dake da zamanta a jihar Legas dai ce ta yi watsi da karar Tonye Cole a hukuncin da ta yanke a ranar 28 ga Nuwamba shekarar 2023, wanda ya yi watsi da daukaka karar da ya yi saboda rashin isasshiyar shaida da kuma gamsassun hujojji.

A wani hukuncin bai daya, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe, inda ta yi watsi da kararraki hudu da dan takarar jam’iyyar APC Tonye Cole da Beatrice Itubo na jam’iyyar Leba, sai Innocent Ekwu na jam’iyyar APM da Lulu Briggs Dumo na jam'iyyar Accord Party suka shigar.

Dan takarar na jam’iyyar APC, wanda ya halarci zaman kotun a yau Alhamis, ya bukaci kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ribas na watan Maris din shekarar 2023.

Kotun Koli Ta Kori Karar Umar Na PDP Tare Da Tabbatar Da Ahmad Aliyu Na APC A Matsayin Gwamnan Sakkwato

Hakazalika, Kotun ta tabbatar da zaben gwamna Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC a jihar Sakkwato jim kadan bayan yin watsi da karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Sa'idu Umar suka shigar.

Dan takarar PDP ya kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar na Sakkwato da aka gudanar a ranar 18 ga Maris shekarar 2023.

Mai shari’a Tijjani Abubakar ne ya karanta hukuncin kotun kolin da ya tabbatar da zaben gwamna Ahmad Aliyu a matsayin zababben gwamnan jihar Sakkwato.

Kotun koli ta amince da hukuncin kananan kotunan da suka hada da na sauraron kararrakin zabe da na kotun daukaka kara a zaben gwamnan jihar Sakkwato, wadda ya yi watsi da karar da aka shigar na neman soke zaben Gwamna Aliyu.

Ahmad Aliyu shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben na ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

A waccan lokaci, bayan gudanar da zaben ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC ta bayyana Aliyu a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta ce ya sami kuri’u dubu 453 da 661, inda ya doke abokin hamayyarsa Umar dan takarar jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 404 da 632.

A bisa rashin gamsuwa da sakamakon zaben, Sa'idu Umar da jam’iyyarsa ta PDP sun shigar da kara a gaban kotun inda suka ce Ahmad Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir ba su cancanci tsayawa takara ba.

Sun kuma yi ikirarin cewa zaben ba kawai mara inganci ba baya ga cewa ba a gudanar da shi bisa tanadin dokar zabe ta shekarar 2022 ba inda kuma suka zargi gwamnan da mataimakinsa da gabatar da takardun bogi masu bambancin suna ga hukumar zabe.

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Kefas Agbu A Matsayin Gwamnan Jihar Taraba

Kotun kolin ta kuma tabbatar da zaben Agbu Kefas a matsayin gwamnan jihar Taraba a yau Alhamis.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta yi watsi da karar da Farfesa Yahaya Sani na jam’iyyar NNPP ya shigar a bisa rashin cancanta.

Farfesa Sani ya bukaci Kotun Koli da ta yi fatali da zaben Agbu Kefas na jam’iyyar PDP, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris na shekarar 2023.

Dan takarar na jam’iyyar NNPP ya yi zargin rashin cewa an ki bin ka’idar dokar zabe da kuma tafka wasu kura-kurai a zaben kuma ya roki kotu da ta soke zaben Kefas tare da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cewar Farfesa Sani, shi ya sami mafi rinjayen kuri’un da aka kada a ranar zabe a jihar Taraba.

Idan Ana iya tunawa, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a watan Nuwambar shekarar 2023 ta yi watsi da karar Farfesa Sani bayan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta tabbatar da zaben Agbu Kefas a matsayin zababben gwamnan jihar Taraba.

A baya dai, kotun daukaka kara a cikin hukuncin data yanke ta yi watsi da karar na Farfesa Sani a bisa rashin cancanta.

A yau Alhamis ne mai shari’a Lawal Garba, wanda ya karanta hukuncin kotun koli ya yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP da dan takararta Farfesa Sani suka shigar.

Idan Ana iya tunawa, dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Taraba Kefas Agbu ya sami kuri’u dubu 302 da 614 inda ya doke dan takarar jam’iyyar NNPP, Muhammad Yahaya wanda ya sami kuri’u da dubu 202 da 277.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG