Hukumar INEC, a wata sanarwa ta ce ta dakatar da jami'in nata ne don samun sukunin gudanar da bincike a kan bacewar takardun kada kuri'a na kujerar majalisar wakilai na shiyyar Bassa da Jos ta Arewa a rumfuna goma sha shida, a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Jami'a a sashen yada labarai na hukumar INEC, Zainab Aminu, ta tabbatar da dakatar da jami'in, don yin bincike.
Duk da umurnin sake yin zaben a ranar Lahadi a wasu rumfuna, jami'an zabe basu fito a kan lokaci ba, yayin da a wasu rumfunan jama'a basu fito don sake gudanar da zaben ba.
Mr. Raphael Madugu, wani dan jarida a jihar Filato, yace sun yi ta kokarin samun jami'in hukumar zaben don yayi bayani kan matsalolin da aka fuskanta a rumfunan zaben amma bai amsa kira da sakonni da aka aike masa ba.
An gudanar da zaben Sanata na shiyyar Arewacin jihar Filato da na majalisar wakilai na Jos ta Arewa da Bassa ne bayan da kotu ta soke wadanda aka zaba a karkashin jami'iyyar PDP, bayan da ta ce jami'iyyar bata da zababbun shugabanni a jihar Filato a lokacin da aka gudanar da zabukan gama gari a shekara ta dubu biyu da ishirin da uku.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna