Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Zaben Cike Gurbi A Wasu Jihohin Najeriya


Malaman zabe a wata mazaba a jihohin da ake zaben cike gibi a Najeriya
Malaman zabe a wata mazaba a jihohin da ake zaben cike gibi a Najeriya

Wasu daga cikin jihohin da aka yi zaben sun hada da Filato, Nasarawa, Kaduna, Binuwe, Ebonyi, Yobe, Ondo, Taraba, Borno, Kebbi da Legas.

A Najeriya, ana gudanar da zabukan cike gurbi da wadanda kotu ta ba da umarni a sake a matakai daban-daban a jihohi 26 da ke kasar.

Wasu daga cikin jihohin sun hada da Filato, Nasarawa da Kaduna, Binuwe, Ebonyi, Yobe, Ondo, Taraba, Borno, Kebbi da Legas.

Zabukan wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ke gudanarwa sun hada da na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a wasu sassan kasar.

Masu kada kuri'a a zaben cike gurbi a Najeriya
Masu kada kuri'a a zaben cike gurbi a Najeriya

Rahotanni sun yi nuni da cewa, an bude rumfunan zabe da wuri a wasu yankunan kasar yayin da aka samu jinkiri a wasu wuraren.

Wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka a Jos, Zainab Babaji, ta ce an yi zaben lami lafiya a jihohin Filato, Binuwe da Nasarawa.

“Sai dai abin takaici shi ne, mutane da yawa ba su fito zaben ba," in ji Babaji.

Masu kada kuri'a a zaben cike gurbi a Najeriya
Masu kada kuri'a a zaben cike gurbi a Najeriya

A jihohin Binuwe da Nasarawa, rahotanni sun nuna cewa har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu wata tangarda kwakkwara ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa hukumomi sun baza jami’an tsaro a sassan kasar da ake zabe domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an dakatar da zaben a wasu rumfuna a jihohin Akwa Ibom, Enugu da Kano saboda hargitsi da magudi da ake zargin an samu a wasu rumfunan zabe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG