Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i Sun Fara Yajin Aiki


Taron manema labarai na kungiar manyan ma'aikatan jami'a reshen jihar Adamawa
Taron manema labarai na kungiar manyan ma'aikatan jami'a reshen jihar Adamawa

Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'i ta kasa reshen jami'ar Jihar Adamawa dake Mubi, ta bi sawun takwararta kungiyar malamai wajen shiga yajin aikin sai baba ya gani, kan abin da suka kira kuntatawa da rashin biyan su hakkokinsu tare da sharadin sai an biya su da kuma sauke shugaban jami'ar daga kan mukaminsa.

Shugaban kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'i ta kasa reshen jami'ar Jihar Adamawa Kwamarad James Kole Fwah, ya bayyanawa taron manema labarai a cibiyar 'Yan jaridu dake Yola fadar jihar Adamawa, cewa shekara biyu ke nan hukumar jami'ar bata baiwa kungiyar kudaden Karo-karo da ake cirewa daga albashinsu ba, karo-karon fansho da kuma kuntatawa mambobinta ta hanyar Korar wasu daga bakin aiki ba bisa ka'ida ba.

Tun lokacin da aka nada shugaban jami'ar inji shugaban kungiyar malaman jami'o'i ta kasa reshen jimi'ar, Kwamarad Abubakar Aliyu Song, sakamakon rashin sanin makamar aiki da ya sa wasu manyan malamai 18 suka yi hijira zuwa wasu jami'o'i na Najeriya.

Da yake kare matsayinsa kan korafe-korafen kungiyoyin, shugaban jami'ar Dakta, Moses Zaruwa, yana zargin wasu daga waje da ya ce su ke ingizasu su bijirewa hukumar jami'ar, inji shi wasu daga cikinsu na gaban kuliya inda suke fuskantar tuhuma da ake yi musu kan zarmiya.

Jami'ar Jihar Adamawa ta fada cikin rudani shekara biyu da suka gabata lokacin da tsohon shugaban jami'ar Farfesa David Joshua Shall da ma'ajinta Mr, Kumthi Ezra Anjili, suka rika yi wa juna tonon silili da kawo yanzu hukumar EFCC ke ci gaba da bincikarsu.

Domin karin bayani saurari rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG