Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Shiryawa Kungiyar BBOG da 'Yan Jarida Ziyara Zuwa Dajin Sambisa


Kungiyar BBOG ko Bring Back Our Girls a turance, da shugabarsu Oby Ezekwesili da Hajiya Aisha Yusuf sanye da hijab a bayan shugabar
Kungiyar BBOG ko Bring Back Our Girls a turance, da shugabarsu Oby Ezekwesili da Hajiya Aisha Yusuf sanye da hijab a bayan shugabar

Jiya wani jirgin saman sojojin Najeriya dauke da jami'an tsaro da 'yan jarida da wasu shugabannin kungiyar BBOG dake fafutikar kwato 'yan matan Chibok ya tashi domin ziyar gani da ido kan yadda dakarun sojojin ke kokarin kwato sauran 'yan matan Chibok su 195.

Tawagar ta BBOG ta hada da jagorarsu Oby Ezekwesili da Hajiya Aisha Yusuf da Manaseh Allen da Ibrahim Usman.

A cewar Ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammed ziyarar ta tsawon wuni biyu ce kuma jirgin dake dauke dasu zai yi shawagi dasu akan dajin Sambisan.

Baicin wakilan kafofin labarai mallakar gwamnatin Najeriya akwai kuma wakilan dillancin labarai na kasashen ketare da suka hada da Reuters da AFP.

Wannan ziyarar gani da ido ita ce ta farko da aka gayyaci 'yan gwagwarmayar BBOG amma dama can manema labarai da hedkwatar tsaro sun saba shirya irin wannan ziyarar.

Sanya 'yan BBOG a wannan karon yana da alaka ne da yadda 'yan kungiyar ke nuna rashin gamsuwarsu da bugun kirjin da sojoji keyi na cewa sun wargaza tungar 'yan Boko Haram dake dajin Sambisa. Kungiyar na ganin idan ikirarin sojojin gaskiya ne to yaya aka yi ba'a samo ko daya daga cikin 'yan matan 195 ba? Haka kuma abun mamaki ba'a gano madugun 'yan ta'adan ba Abubakar Shekau wanda kusan kullum yana magana.

A cewar daya daga cikin jigajigan kungiyar BBOG Dr. Emmanuel Shehu har yanzu jami'an tsaron Najeriya basu fahimci abun da ake nufi da dimokradiya ba. Har yanzu suna nan da tunanen lokacin da sojoji suka yi mulkin kasar. Yace saboda haka akwai sauran aiki a kasar musamman akan yadda yakamata jami'an tsaro suyi mua'amala da mutanen kasarsu a karkashin mulkin dimokradiya.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG