Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar Da Najeriya Za Ta Taka a Zaman Lafiyan Gambia


Shugaba Mohammadu Buhari da Yahya Jammeh
Shugaba Mohammadu Buhari da Yahya Jammeh

Ranar Laraba 18 ga watan Janairu wa’adin mulkin shugaban Gambia Yahya Jammeh ke karewa, kuma babu alamun zai mika mulki ga sabon zababben shugaban Adama Barrow mulki.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, shine kan gaba wajen neman masalahar diflomasiyya bisa jagorantar tawagar kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, da ta ziyarci Banjul har sau biyu ba tare da shawo kan matsalar ba.

A halin yanzu dai Adama Barrow ya daura aniyar za a rantsar da shi bayan 18 ga wata, duk da yanzu dai yana zaman jira ne a kasar Senegal. Shugaban asusun Macarthur a Najeriya, mai raya ilimi da dimokaradiyya Dakta Kwale Shettima, yace zabin amfani da karfin soja ba zai harfar da riba ba.

Wanda kuma ya bayar da shawarar gwamnatin rikon kwarya ko ta hadaka, kamar yadda ya faru tsakanin tsohon shugaban Kenya Mwai Kibaki da Raila Odinga, bayan rikicin zaben a shekara ta 2008.

Shin idan har sai soja sun shiga lamarin Najeriya ka iya zama jagaba? A tarihi dai Najeriya ta tallafa wajen dawo da zaman lafiya a yakin basasar Laberiya da Saliyo, har ma da tura dakaru wajen kawo zaman lafiya a Sudan. Duk kuwa da Najeriya ta bayar da goyon baya wajen dasa dimokaradiyya a Côte d’Ivoire amma Faransa ce tayi jagaba wajen ture tsohon shugaba Laurent Gbagbo da ‘daura zababben shugaba Alhassan Watara.

Haka nan kuma Faransa ce ta yi ja gaba wajen kawar da gwamnatin Ajwad ta ‘yan tawaye a Mali. Karfin soja da na dimokaradiyya zasu karawa Najeriya tagomashi a Afirka, kamar yadda Amurka take a fadin Duniya.

A kungiyace ECOWAS ce zata yanke matsaya kamar yadda ta matsa lamba kamar yadda ta matsa lamba wajen hana tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou ci gaba da mulki a wa’adi na uku.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG