Yau ne shugaba Muhammadu Buhari zai fara ziyarar aiki na kwanaki uku a Kasar Kenya, inda zai halarci taron jajen kisan Sojojin Kenya da kungiyar nan ta ‘yan ta’adda na al-Shabaab, na Somalia suka yi a ranar 15, wannan watan, daga bisani zai halarci wasu tarurruka difilomasiya, da bunkasa kasuwanci tsakanin Kenya da Najeriya.
Daga bisani ne shugaba Muhammadu Buhari, ake sa ran zai halarci taron kasashen Afirka wanda za’a yi Addis Ababa, ta kasar Ethiopia, domin tattauna abubuwan dasu hada da cinikayya da tsaro.
Kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, yace ita wannan ziyara ta Kenya, ziyara ce ta ‘yan uwantaka, kuma ganin cewa kasashen na da matsaloli iri daya Kenya, na fama da al-Shabaab, Najeriya da Boko Haram, saboda haka akwai maganar tsaro da za’a tattauna ta yadda za’a yi magani shigar makamai irin kasashen mu domin ayi barna dasu.
Ya kuma kara da cewa yaki da cin hanci da rashawa, da ake yi a Najeriya, sauran kasashen Afirka, suma zasu ci gajirar shi, kamar yadda kasashen duniya suke sa ido kan abunda akeyi a Najeriya, suna yabawa kuma suna kafafa guiwar ayi.