Suma yaran makaranta ba a barsu a baya ba domin kuwa daukacin makarantu duk sun kasance a kulle suna hutun zubar dusar kankarar da aka dade ba a ga irinta a kasar ba.
Duk da kokarin da gwamnati tayi na ganin ta share manya-manyan tituna a ciki gundumar ta Colombia da jihar Maryland har, yanzu akwai wasu titunan da dusar kankaran take jibge kamar ba a dibarta.
Wanda hakan kuma ya haifar da cunkoson motoci a wasu sassan biranen. Jiragen sama da suka kai 1500 ne aka hana tashi da sauka a tashoshin jiragen saman garuruwan da suka hada Washington da Baitimore da New York da kuma Philadelhia duk a jiya Littinin.
Yayin da jiragen kasa suka fara aiki a hankali kuma kyauta aka shiga. Wannan dusar kankarar dai tasa mutane da yawan gaske a birnin New York kauracewa birnin zuwa kudancin jihar.
Inda kankarar ta fi zuba matukar gaske sune garuruwan na Baltimore da da kuma Washington. Yanzu dai abubuwa sun fara komawa dai-dai, duk da yake ana ganin tari-tarin dusar kankarar a sassa da dama na wuraren da ta yiwa dirar mikiya.