Da yake jawabi a wurin wani babban taron da akayi wata Kwalejin Koyon Dabarun Yaki a Abuja, babban Hafsan tsaron Najeriya, yace dangane da masu tayar da kayar baya na ‘yan Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas, yanzu fada ya kare saura shara.
Olonishakin yace, “mun gama da su, yanzu muna kokarin ganin mun tabbatar da karkade ‘dan guntun kurar da ta rage, kana mu tunkari sauran ‘dan abinda ba za a rasa ba daga da ka iya tasowa a wannan shiya. Ya ci gaba da cewa na tabbata kuna sane da batun wadanda tarzoma ta raba su da gidajensu.”
A daya bangaren kuma daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron ‘kasa, Burgediya Janaral Rabe Abubakar, ya kara tabbatar da cewa nan gaba kadan za a kammala ‘dan abinda ya rage na wannan fafatawa. Ya kuma nemi mutane da su rika basu bayanan sirri da zai taimaka musu wajen gudanar da aikinsu kamar yadda ya dace.
Shima Kanar Aminu Isa Kwantagora, tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, kuma kwararre wajen sha’anin tsaro. Ya nemi mutane da su shirya domin masu tayar da kayar baya ka iya kai hari jifa jifa, to dole ne mutane su saka ido. saurari cikakken rahotan.