Domin kuwa kullum suka tashi aiki suna garzayawa ne su koma inda suka kama gidaje da dakunan hayarsu wanda ke unguwannin wajen birnin. Domin kuwa akwai da yawa da suka kakkama gidaje a garurun dake ke makwabtaka da birnin tarayyar Najeriyar.
Ma’ana kamar su Suleja da ke jihar Neja da irin su Nyanya da ke jihar Nasarawa, wadda mutanen da basu san bambanci ba ma gani suke yi duk garuruwan suna karkashin Abuja ne. Saboda haka da safiya ta yi zaka ga ma’aikata na ta tururuwa zuwa ciki Abuja, haka ma da sun tashi aiki zasu yi ta karakainar komawa gidajensu.
Wannan ce ta kan sa sai kaga kafin shigowar ma’aikata ofisohinsu ko kuma bayan sun tarwatse zuwa makwantinsu, sai ka ji garin na Abuja tsit kamar ba jama’a. domin kuwa duk an dade an barta. Idan ka debe masu hannu da shuni da manyan jami’ai da ma’aikatan gwamnati ba mai iya zaman hayar cikin birnin.
Don kuwa akalla kana bukatar akalla Naira Miliyan daya da rabi in kana bukatar gida mai daki daya da falonsa a unguwanni irin su Asokoro ko Maitama da Wuse II. Ko mai dakuna biyu a irin su Gwarimpa da Zuba da Lugbe a shekara.
Sabon Ministan Abuja Muhammadu Musa Bello ya bayyanawa wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya yadda zasu shawo kan matsalar wannan tsadar gidajen haya da ke watsa ma’aikata daga cikin birnin wanda hakan ke haifar da matsalar cinkoson motoci wajen turmutsutsun shiga zuwa ma’aikatunsu ko kokarin ficewa daga garin bayan tashi daga aiki.
Ministan y ace zasu bunkasa kananan hukumomin Abuja guda shida ta hanyar samar da saukakaukun gidajen da zasu zamewa ma’aikata mafitar da zasu iya zama cikin garin don rage cinkoso da zafin rayuwa.