Masana harkokin lafiya a Najeriya su na danganta yawan haihuwar jarirai babu rai a kasar a kan yadda mata masu yawa ba su zuwa wurin awu a lokacin da suka dauki juna biyu domin a gano ko su na da wata matsalar da zata bukaci a kula da su kafin haihuwarsu.
Wannan ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa Najeriya ce ta biyu a bayan kasar Indiya, wajen yawan haihuwar jariran da ba su fitowa da rai.
Dr. Grema Bukar na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Aminu Kano, yace akasarin mata, musamman a yankunan karkara, ba su zuwa asibitoci domin yin awu, a saboda dalilai masu yawa.
Yace babban dalilin da yasa ake bukatar mace ta gaggauta zuwa awu da zarar ta samu ciki, shine don a gano ko tana da wasu abubuwan da zasu iya shafar lafiya da kuma ranta da na abinda take dauke da shi a ciki. Musamman yace likitoci su na son su gano ko mace tana da ciwon sukari ko na hawan jini, sannan kuma ko tana da wani ciwon da zai iya shiga jikin jaririn nata.
Dr. Grema yace ciwon sukari da na hawan jini, yanzu sun zamo ruwan dare, ba kamar can baya ba. Daukar matakan rage hawan jini da sukari a jikin mace mai ciki, na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa mace ba ta haifi da ba rai ba, ko kuma ita kanta ta rasa ranta a lokacin haihuwa ba.
Yace a lokacin awu na farko da na biyu, nan ake tantance mata masu juna biyu, a ware wadanda watakila ba zasu bukaci kulawa ta musamman ba, da kuma wadanda za a yi ta kula da su har zuwa lokacin da zasu haihu.