A wajen taron manazarta sun mayar da hankali ne akan hanyoyin aikin noma zai samar da isasshen abinci da kuma arziki ga ‘yan kasar ta Najeriya wadanda talauci yayiwa katutu.
Shugaban jami’ar Musulunci ta Al’kalam dake Katsina Farfesa Shehu Garki Ado, ya bayyana cewa babu yadda za a samu bunkasar tattalin arziki a Najeriya, mudddin ba a sarrafa kayayyakin da ake nomawa musamman a arewacin Najeriya.
Mai alfarma sarkin musulmi Mohammad Sa’ad Abubakar iii, shine babban mai masaukin baki, ya bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da ire-iren wannan takukan tare da masana da kwararru amma daga bisani babu wani tasiri da zasu harfar.
A cewar shugaban cibiyar addinin musulunci ta Najeriya Dakta Mohammad Babangida Mohammad, musulunci al’amari ne mai fadi wanda ya hada da duk wani abin da ya shafi rayuwar ‘dan Adam. Hakan yasa yake daga cikin koyarwar addinin musulunci a janyo hankalin shugabanni bisa hanyar da zasu taimakawa talakawansu fita daga cikin kuncin da suka tsinci kansu ciki.
Taron dai yayi matsayar cewa wajibi ne a sami hadin kai tsakanin al’ummar Musulmai mabiya akidu daban-daban, da ma ‘yan Najeriya baki ‘daya dake da addinai iri daban-daban domin samun ci ga mai dorewa.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk.
Facebook Forum