A bana dai jama’a da dama sun rungumi harkar noma, musamman noman rani a wani yunkuri na yaki da talauci da yunwa
Manazarta dai na gargadin cewa a bana akwai yuwar samun ruwa mai yawa da ka iya kawo ambaliya.
Ambaliyar ruwan ta yi barna a gonakin shinkafa da sauran amfanin gona da ake nomawa a yankin Nyokkore dake kusa da Geriyo dake da dubban gonakin noman rani a jihar Adamawa.
Yanzu haka ma dai wannan ibtila’in ambaliyar ya jefa manoma da dama cikin mawuyacin hali, kuma wannan na zuwa ne dai dai lokacin da aka fara girbe kan amfanin gona da aka noma, kamar yadda manoman suka tabbatar.
Haka shima da yake Karin haske Sarkin ruwan Geriyo Abdurrazaq Abubakar, yace rabonsu da su ga irin wannan ambaliyar an kwashe shekaru, wanda haka nema ya yi kira ga gwamnati data kai musu dauki.
Kawo yanzu tuni gwamnatin jihar ta tura wata tawaga domin ganewa idanuwanta irin barnar da ambaliyar ta jawo a cewar Waziri Ahmadu, kwamishinan harkokin noma a jihar Adamawa.
To sai dai kuma, yayin da wannan ambaliyar ke faruwa a bana dai jama’a da dama sun rungumi harkar noma, musamman noman rani a wani yunkuri na yaki da fatara da yunwa, to wai ko me gwamnatin jihar ke yi ne don tallafawa manoman? Gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla, yace suna sane da manoman ka iya fadawa don haka suka dau mataki.
Manazarta dai na gargadin cewa a bana akwai yuwar samun ruwa mai yawa da ka iya kawo ambaliya, wanda kuma da fatan za’a kula!
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum