Yanzu haka dai allura na neman tono garma game da makudan kudade na biliyoyin Naira da hukumar EFCC ta gano a wani gida a birnin Legas, wanda kuma hukumar NIA, tace kudaden nata ne.
Gwamna Ayodele Fayose, na jihar Ekiti yace abin akwai ban mamaki yanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa zata kama makudaden kudade sannan wata hukuma ta gwamnati tace wadannan kudade nata ne, kuma batare da gwamnatin Muhammadu Buhari mai ikirarin yaki da cin hanci da rashawa tace komai ba.
Gwamnan na Ekiti, wanda yayi suna wajen sukar gwamnatin Muhammadu Buhari, yace kalaman na hukumar NIA na tabbatar da zargin da suke yi tun farko cewa babu wani yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin APC, keyi illa yaki da ‘yan adawa da neman mayarda kasar mai jam’iyya daya tilo.
A yadda ake ci gaba da saurare da kuma kallon wannan badakala ‘yan Najeriya sun fara nuna shakku da kalaman hukumar NIA, wace kuma aka dade ba a ji duriyarta.
Yanzu dai abun jira a gani shine matakin da fadar shugaban kasa zata dauka na shawo kan wannan lamari, tuni itama gwamnatin jihar Rivers tace kudaden nata ne da take zargin tsohon gwamnan jihar kuma na hannun damar shugaba Muhammadu Buhari, watau Ministan sifiri Rotimi Amechi, ya wawure a lokacin da yake gwamnan jihar ta Rivers.
Facebook Forum