Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Akwai Masu Shakka A Batun 'Yan Matan Chibok


'Yan Matan Chibok
'Yan Matan Chibok

Hanyar tattaunawa da 'yan Boko haram zai yi tasiri wajen sako sauran 'yan matan da ake tsare dasu

Baya ga lacca da juyayi da ‘yan kungiyar neman ceto ‘yan matan Chibok watau BBOG, suka yi sun karfafa muhimmacin tattaunawa da ‘yan ta’adda wajen samo sauran matan dari da tasa’in da biyar.

Kungiyar na da ra’ayin mata ashirin da daya sun samu ne ta hanyar tattaunawa inda uku ne kacal suka kubuto ko kuma domin amfani da kafin Soja.

Sakatariyar kungiyar Aishatu Yesufu, tace a watan Oktoba na shekarar 2016, a lokacin da aka sako ‘yan mata ashirin da daya gwamnati tace akwai ‘yan mata tamanin da uku wanda bada dadewa ba za a fito dasu amma har yanzu babu labara.

A nata bangaren wata ‘yar kungiyar Maureen Kabruk, tayi zargin kasancewar mata ‘ya’yan talakawa ne shi yasa tun zamanin gwamnatin Jonathan ba a dage kwarai wajen ceto su ba.

Dr. Manasseh Allen, wakilin al’umar Chibok, a kungiyar, wanda ya yabawa kungiyar akan irin kokarin da take yi, yace duk da wannan fafutukar da akeyi har yanzu akwai mutanen da basu yarda cewa wasu ‘yan mata sun bata ba.

Kungiyar ta yabawa gwamnatin wajen samawa jami’an tsaro masamma Soja sama kaya yakin murkushe Boko Haram. Gwamnatin Najeriya dai tace tana yin duk abu mai yuwa domin dawo da sauran ‘yan matan, da shedawa 'yan kungiyar su zama masu karfin guiwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG