A yanzu dai rundunar sojoji tana ci gaba da kimtsa jami'anta bisa tanadin da kundun tsarin mulkin Najeriya ya yi domin taimaka wajen tunkarar matsalolin fashi da makami, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri da fadan kabilanci da na addini tare da kuma rikicin Makiyaya da Fulani a kudancin jihar Kaduna, inji Manjo Janar David Ahmadu.
Shirin Operation Harbin Kunama kashi na biyu zai samar da cikakkiyar nasarar fataktakar 'yan Boko Haram kwatakwata daga dajin Sambisa.
Rundunar zata yi taro da fararen hula masu ruwa da tsaki a Kafanchan jihar Kaduna da Ganawuri dake jihar Filato. Sojojin sun kuma ja hankalin mutanen Kano, Kaduna, Filato da Bauchi kada su razana lokacin da suka ga manyan mayaka suna cikin damar yaki suna kaiwa da kawowa.
Abubakar A Tsanni Mabudin Borgu daraktan wata kungiyar kishin kasa ya yabawa sojojin ya kuma nemai jama'a da su bada hadin kai domin cimma manufar tsaro.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum