Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAFDAC Ta Rufe Kasuwar Magani Ta Maiduguri Sakamakon Mummunar Ambaliyar Ruwa


NAFDAC
NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta rufe kasuwar magani ta Gomboru dake birnin Maidugurin jihar Borno, inda aka wanke tare da shanya gurbatattun magunguna a rana domin sake sayar dasu ga jama’a sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa jihar.

Sakon da NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ya bayyana cewa hukumar ta ba da umarnin rufe kasuwar ne sakamakon ambaliyar ruwan da ta shanyeta, kuma magungunan suka gurbace.

“Bayan ambaliyar baya-bayan nan a birnin Maiduguri da ta shafe kasuwar magani ta Gomboru inda aka wanke tare da shanya magunguna a rana domin sake sayar dasu, shugabar hukumar NAFDAC ta ba da umarnin rufe kasuwar nan take domin bada damar bi shago-shago a kwashe gurbatattun magungunan,” NAFDAC ta wallafa.

Fashewar madatsar ruwa ta Alau ce ta haddasa ambaliyar.

Mummunar ambaliyar ta yi sanadiyar salwantar da akalla rayuka 30 tare da tilastawa mutane dubu 400 barin gidajensu.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla fursunoni 286 ne suka arce daga gidan yarin Maiduguri mai matsakaicin tsaro sakamakon mummunar ambaliyar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG