Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Bada Gudunmowar $6M Ga Wadanda Ambaliyar Maidugri Ta Shafa


Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)
Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da gudunmowar dala miliyan 6 a matsayin tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwan birnin Maiduguri ta shafa.

A sanarwar da ya fitar a yau Talata, jami’in kula da harkokin jin kai na majalisar dake Najeriya, Muhammad Fall, yace wata tawagar hadin gwiwa ta jami’an Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu da reshen Najeriya na kungiyar bada agaji ta Red Cross, sun ziyarci birnin Maiduguri a karshen makon daya gabata.

A cewarsa, tawagar ta gana da mutanen da iftila’in ya shafa-galibinsu sun fuskanci matsalar rabuwa da muhallansu sau da dama sakamakon rikici da rashin tsaro a yankin.

Tumbatsar da madatsar ruwa ta Alau dake da tazarar kimanin mil 10 daga kudancin birnin Maiduguri ce ta haddasa ambaliyar.

A cewar mai magana da yawun Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Steven Dujarric yace jami’an ofishin harkokin bada agaji na majalisar na aiki kafada da kafada da kungiyoyin bada agaji domin samo karin kudade.

Ambaliyar ruwa ta lalata fiye da hekta dubu 125 ta kasar noma a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG