Kwamishinan kula da Ma,aikatar kananan Hukumomi da Masarautun jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ne ya tabbatar da wannan adadlin a hirar shi da Muryar Amurka.
A bayaninsa, yace masu zaben sabon Sarkin sun zabi galadiman Kontagora domin ya shugabanci shirin zaben sabon sarki, yayinda aka kara wa'adin rufe karbar takardun neman kujerar sarautar zuwa Jumma, domin ba masu sha'awa da suke nesa damar shigar da takardunsu.
voahausa.com/a/sarkin-sudan-na-kontagora-alhaji-shehu-namaska-ya-rasu
voahausa.com/a/yadda-yan-bindiga-suka-kashe-sardaunan-kontagora-a-jihar-neja
A nasa bayanin,shugaban masu zaben sabon sarkin mai daraja ta daya, Alhaji Shehu Yusuf Galadima, yace zasu gudanar da aikinsu tsakani da Allah ba tare da jin tsoron saka bakin wwamnati ba. Bisa ga cewarsa, gwamnati takan shiga batun zaben sabon Sarki ne idan ta ga an tauye hakin wani ko kuma an nuna rashin adalci.
Bisa ga cewarsa, suna da hakkin zaben Sarkin da zai zama karbabbe wanda al'ummar masarautar su ke so domin ci gaban masarautar da kuma jihar baki daya.
Yanzu Hankali ya karkata tare da jiran Lokaci domin gani wanda zai zama sabon sarki a masarautar ta Nagwamatsen.
An haifi tsohon Sarki Alhaji Sa'idu Namaska a shekarar 1937, ya kuma hau karagar mulki a shekara ta 1974. ya kasance barasaken da ya fi kowanne dadewa bisa karagar mulki a arewacin Najeriya.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: