Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Sarkin Kagara A Jihar Nejar Najeriya


Sabon Sarkin Masarautar Kagara da ke Jihar Nejan Najeriya, Alhaji Ahmed Garba Gunna
Sabon Sarkin Masarautar Kagara da ke Jihar Nejan Najeriya, Alhaji Ahmed Garba Gunna

Sabon sarkin Alhaji Ahmed Garba Gunna, ya nemi hadin kan al’ummar masarautar wajen shawo kan babbar matsalar da ke ci wa masarautar tuwo a kwarya, wacce ta shafi rashin zaman lafiya.

Gwamnatin jihar Neja ce ta sanar da nadin Alhaji Ahmed Garba Gunna a matsayin sabon Sarkin Kagara.

Hukumomin jihar sun fitar da wannan sanarwar ce bayan amincewa da zabin da masu zaben Sarki a masarautar Kagara suka yi, wajen tabbatar da Alhaji Gunna a matsayin sabon sarki a cewar kwamishinan kula da Masarautu, Barista Abdulmalik Sarkin Daji.

Kafin wannan nadi, Alhaji Ahmed Gunna, shi ne ke rike da mukamin mai girma Dan Majin Kagara. Kuma bisa bin dokar nadin sabon Sarki, ya samu kuri’u biyar na masu zaben Sarki a masarautar, domin zama sabon Sarkin Kagara.

Sabon Sarkin Masarautar Kagara da ke Jihar Nejan Najeriya, Alhaji Ahmed Garba Gunna
Sabon Sarkin Masarautar Kagara da ke Jihar Nejan Najeriya, Alhaji Ahmed Garba Gunna

Mai martaba sabon sarkin ya nemi hadin kan al’ummar masarautar domin shawo kan babbar matsalar da ke ci wa masarautar tuwo a kwarya, wanda shi ne rashin zaman lafiya.

Haka kuma ya sha alwashin janyo dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da samar da ci gaba a Kagara.

A ranar daya ga watan Maris din da ya gabata ne Allah ya yi wa tsohon Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko rasuwa, sakamakon fama da rashin lafiya, bayan da ya kwashe kimanin shekara talatin da biyar akan karagar mulki.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG