Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyan Zazzau Bashir Aminu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya


Iyan Zazzau Bashir Aminu
Iyan Zazzau Bashir Aminu

Da safiyar yau Allah ya karbi ran Iyan Zazzau Alh. Bashir Aminu, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un! Allah ya yi wa Alh. Bashir Aminu Iyan Zazzau rasuwa.

Babban dan margayin Dr. Nasiru Bashir Aminu, ya shaidawa Muryar Amurka da rasuwar mahaifin nasu. Iya Bashir ya yi fama da rashin lafiya na gajeren lokaci. A makon da ya gabata ne dai ya cika shekaru 70 a duniya, ya rasu ya bar matan aure 4, da 'ya'ya 34, kana jikoki da dama.

Iyan Zazzau Bashir Aminu
Iyan Zazzau Bashir Aminu

Margayi Iyan Zazzau, ya shigar da kara akan abun da ya kira rashin adalci, bayan sake zaben sarkin Zazzaun da aka yi, wanda ya nemi sararutar, Idan ba'a manta ba dai Sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris, ya rasu a watan Satumbar shekarar 2020.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG