Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 sun Mutu a Turkiyya Bayan wata Arangama da 'yan Sanda


Zanga-zanga a Diyarbakir, Turkiyya, 9 ga Oktoba, 2014.
Zanga-zanga a Diyarbakir, Turkiyya, 9 ga Oktoba, 2014.

Wasu mutane 12 a kalla sun mutu a kasar Turkiyya bayan wata arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Kurdawa.

Wasu mutane 12 a kalla sun mutu a kasar Turkiyya bayan wata arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Kurdawa, wadanda ke neman gwamnatin kasar ta taimakawa Kurdawa a makwafciyar kasar Siyria su yaki mayakan Daular Islama.

Mutane takwas sun mutu a jiya Talata a babban garin Kurdawa na Diyabakir a kudancin kasar Turkiyya, ayayin da sauran kuma suka mutu a Mus, da Siirt da kuma Batman.

A makon da ya gabata majalisar dokokin kasar Turkiyya ta bada izinin yin amfani da karfin soja a kan kungiyar Daular Islama a Iraki da Syria, amma sojojin kasar ba su tsallaka kan iyaka sun kai dauki cikin birnin Kobani na kasar Syria ba, wanda kuma ake kira Ayn al Arab.

Mayakan Kurdawa sun yi makonni suna gwabza yaki da 'yan tawayen Daular Islama. Shugaban kasar Turkiyya ya fada a jiya Talata cewa nan kusa za a kwace garin ba tare da taimakon mayakan kasa ba.

XS
SM
MD
LG