Hukumomin Amurka sun kama wani dan kasarta dan shekaru 19 da haifuwa kan zargin yana kokarin tafiya kasashen waje domin ya shiga kungiyar ISIS.
A cikin wata sanarwa data bayar jiya Litinin, ma’aikatar harkokin shari’a tace jami’an FBI sun kama Mohammed Hamzah Khan ba tareda wata turjiya ba ranar Asabar a babbar tashar jiragen sama ta kasa da kasa a O’Hare dake Chicago,kan hanyarsa zuwa Istanbul, amma zai yada zango a Vienna.
Jiya Litinin aka shigar da kara gaban kotu inda ake tuhumarsa da laifi daya na kokarin taimakawa kungiyar ta’adanci a ketare wacce take gudanar da harkokinta a Iraqi da Syria. Khan wanda yake da zama a jihar Illinois jiyan ya bayyana gaban wani alkalin majistiret, kuma ana ci gaba da tsare shi kamin zaman kotun na gaba ranar Alhamis mai zuwa.
Sanarwar tace kokarin taimakawa kungiyoyin ta’adanci yana dauke da hukuncin daurin shekaru 15 a gidan fursina da kuma tarar dubu metan da hamsin.