Jiya Talata mutum daya ya mutu a kudu maso gabashin kasar Turkiya yayin da ‘yansanda suka kara da daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan kurdawa.
Suna zanga zangar ne akan kin gwamnatin Turkiya ta tura dakatunta su taimaki kurdawan birnin Kobani a kasar Syria dake kan iyaka da kasar Turkiyan.
Kafofin labarum kasar Turkiyan sun bada rahotannin dake karo da juna akan mutuwar mutumin. Wasu sun ce an harbeshi ne wasu kuma sun ce gwangwanin barkonon tsohuwa ya sameshi a kokarin tarwatsa masu zanga zangar a birnin Mus.
Yansanda sun kara da masu zanga-zanga jiya a biranen Istanbul da Ankara.
Kurdawa dai suna rokon gwamnatin Turkiya ta kutsa cikin birnin Kobani dake arewacin Syria kan iyaka da kasar inda mayakan kurdawa suka kwashe mako uku suna fafatawa da mayakan ISIS.
Shugaban Turkiya yace birnin zai fada hannu mayakan ISIS idan sojojin kasa basu kai doki ba.
Makon da ya wuce majalisar dokokin Turkiya ta amincewa gwamnatin kasar tayi anfani da soji a kasashen Syria da Iraqi inda ‘yan Sunni masu tsatsauran ra’ayi suka kwace yankuna da dama wannan shekarar.
To amma har yanzu sojojin Turkiya basu bar inda suka ja daga ba daga iyaka da birnin Kobani wanda kuma ake kira Ayn al-Arab