Fadar White House tace akwai iyakacin irin aikin da sojojinta zasu iya yi su hana kungiyar Islama ta ISIS cafke birnin Kobani dake kan iyaka a kasar Syria.
Mai Magana da yawun gwamnatin Amurka John Earnest ya fada jiya Laraba cewa ba sojojin kasa a Syria kamar a Iraqi inda hare-haren da Amurka ke kaiwa suka taimaki Iraqi da dakarun Kurdawa fatartakar kungiyar ISIS.
Earnest yace rashin sojojin kasa a Syria sun takaita tasirin hare haren da Amurka ke kaiwa akan sansanonin mayakan ISIS a Syria.
Mayakan Kurdawa suna fama da fafatawa da mayakan ISIS domin kada birnin Kobani wanda ake kuma kira Ayn al-Arab ya fada hannunsu.
Yakin da suke gwabzawa yayi sanadiyar dubun dubatan mutane barin gidajensu suna tsallakawa cikin kasar Turkiya domin tsira da rayukansu.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry yace shawarar a kafa tudun natsira akan iyaka, shawara ce da yakamata a duba da idon basira.
Kasashen Faransa da Birtaniya su ma sun goyi bayan shawarar.
To amma Fadar White House tace wannan shawarar bata ma cikin tunaninta