Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Daular Islama ta Kakkabo Wani Karamin Jirgin Sama


Serekaniye, Rojava.
Serekaniye, Rojava.

A karo na biyu, cikin mako daya, mayakan kungiyar Daular Islama sun kakkabo wani karamin jirgin saman sojojin Iraki a kusa da matatar mai mafi girma a kasar.

A karo na biyu, cikin mako daya, mayakan kungiyar Daular Islama sun kakkabo wani karamin jirgin saman sojojin Iraki a kusa da matatar mai mafi girma a kasar, kuma matukan jirgin dukan su biyu sun mutu.

Tun watan Yuni sojojin gwamnatin kasar Iraki ke gwabza yaki da kungiyar ta masu tsattsauran ra'ayi a kan wannan wuri dake birnin Baiji.

A makwafciyar kasar Syria kuma, Kurdawa mayakan sa kai, wadanda kawancen taron dangin kasa da kasa ke tallafawa ta sama da jiragen yaki, sun yi nasarar hana mayakan Daular Islama shiga garin Kobani, kamar yadda aka bada rahoto.

Fadan na makonni uku, wanda ake fafatawa don neman kwace garin na arewaci a kan iyakar Syria da Turkiyya, ya na kara zafafa, a daidai lokacin da mayakan Daular Islama ke kara kusantar garin daga bangarorin da dama.

Mayakan Kurdawa sun bukaci taimakon kasa da kasa wajen kare yankin wanda kuma ake kira Ayn al Arab.

Manzon MDD na musamman a kasar Syria na kashedin cewa mayakan Kurdawa sun kusa kasa iya tsayawa su fuskanci 'yan tawayen na Daular Islama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG