Hukumomin kasar Somaliya sunce mutane shidda sun rasa rayukansu, bayan da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab suka kaiwa wani sansanin soja a wajen garin Baidoa hari.
Shedun gani da ido sun fadawa sashen Somaliya na nan Muryar Amirka cewa wasu 'yan bindiga ne suka kaiwa wani wurin binciken soja hari da sanyin safiyar jiya Juma'a.
Mutane goma sha takwas ne suka ji rauni a fafatawar da aka yi, baya ga mutane shidda da suka mutu. Dukkan bangarorin biyu sun jikatta.
Birnin Baidoa yana tazarar kiamin kilomita maitan da arba'in da biyar yamma da Mogadishu, baban birnin kasar Somaliya.
Motar da aka yi amfani da ita wajen kai harin, mota ce da aka saba amfani da ita wajen jigilar Malamai akan hanyarsa ta zuwa wata makarantar sakandare dake yankin.
Bubu kungiyar data fito tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin na Galkayo.