A Somaliya rundunar dakarun hadin gwiwar kasashen Afirka wato AU ta bayyana cewa mutane 9 ne suka rasa rayukansu biyo bayan wani hari da mayakan al-Shabab suka kaiwa sansaninsu a kusa da babbar tashar jirgin sama na kasa da kasa a Mogadishu.
Rundunar dake ayyukan wanzar da zaman lafiya a Somaliya ko AMISOM a takaice, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa mayakan al-Shabab sanye da kayan sojojin Somaliya suka haura zuwa harabar sansanin da rana jiya Alhamis.
Sanarwar ta kara da cewa mayaka biyar, tare da sojojin AU guda 3 da wani farin hula daya ne suka rasa rayukansu a harin, sannan an cafke wasu mayakan al Shaban guda uku.
Rundunar AMISOM ta bayyana cewa yanzu haka tana rike da ikon sansanin, kuma ayyuka sun cigaba kamar yadda suka saba.
A lokacin da take daukar alhakin harin, kungiyar al Shaban tace manufarta shine kaiwa wani taron shakatawa hari a sansanin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa kungiyar tayi ikirarin kashe mutane 14.