A Somaliya, wani dan kunar bakin wake da mota, ya kashe akalla mutane hudu.
Wani kakakin ma'aikatar tsaron kasar ya gayawa Muryar Amurka cewa, jami'an tsaro sun zagaye motar a wata gunduma da ake kira Waberi da take kusa da babbar tashar saukar jiragen sama ta kasa da kasa dake Mugadishu, a lokacin ne dan harin kunar bakin waken ya tada nakiyoyi da suke cikin motar.
Jami'in yace fashewar ta hallaka fararen hula hudu tareda shi maharin. Wasu mutane akalla biyar kuma sun jikkata.
Mazauna yankin sun kara da cewa, sai kuma harbe harbe da bindiga suka biyo baya.
Kungiyar al-shabab ta dauki alhakin kai harin na jiya Lahadi. A baya bayan nan kungiyar ta zafafa kai hare hare a Mugadishu fadar gwamnatin kasar.
Ranar Alhamis ta makon jiya, wani kwamandan kungiyar ta al-shabab Ibrahim Filey, da wasu mayaka uku sun gamu da ajalinsu a wata arangama da suka yi da sojojin kasar a garin Kurtun Waarey, dake kudancin kasar.