Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tunisia Ta Yi Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa

Dan takarar shugaban kasa Baji Caid Essebsi yana jefa tashi kuri'ar

A kokarin shirinta na komawa tafarkin dimokradiya

Jiya Lahadi aka yi zaben fidda gwani na shugaban kasa a Tunisia, a kuri'ar da ake kallo a zaman mai muhimmanci a yunkurin da kasar take yi na komawa bin tafarkin demokuradiyya.

Ba a dai bada kwarya-kwaryar sakamakon zaben ba, amma jam'iyyar dan takarar da ake kira Beji Caid Essebsi, wacce take adawa da jam'iyun addini, a gurguje ta ayyana kanta a matsayin wacce ta lashe zaben kan abokin takararsa, shugaban kasar na wucin gadi, Moncef Marzouki. Manajan kamfen din Essebsi, yace sakamakon farko farko wanda ba a hukumance ba, ya nuna cewa Beji wanda tsohon minista ne dan shekaru 88 da haifuwa ne, ya sami nasara.

Amma a nasa martanin, manajan kamfen na shugaban kasar na wucin gadi, yayi watsi da ikirarin abokin takararsu, yana cewa da wuya wani yanzu haka yayi ikirarin shi ya sami nasara.

Zaben na jiya shine rukuni na karshe a shirin komawa turbar demokuradiyya, tun bayan juyin juya halin da aka yi a kasar a 2011, wanda yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin mutumin da ya juma yana mulkin kasar Zine El-Abidine Ben Ali.

Lamarin da aka lakabawa bazarar larabawa, da wasu suka kwai-kwaya a yankin.

XS
SM
MD
LG